Shahararren mawakin nan, jarumi, mai shirya-fina finai kuma Umar M. Shareef ya bayyana cewa soyayya ce musabbabin dalilin fara rera wakar shi a matsayin sana'a. Wannan ne ma yasa a cewar ta sa jama'a ke ganin kamar yafi maida hankalin sa wajen yin wakokin da suka shafi soyayyar a cikin fina-finai.

Sabon jarumin, Umar M. Shareef ya yi wannan bayanin ne a cikin wata tattaunawa da yayi a wani gidan radio inda kuma ya bayyana cewa ya fara rera waka ne a lokacin da yake jiran ansar wata yarinyar da yace mata yana son ta, bata dawo ba.

KU KARANTA: Hadiza Gabon na daf da zama amarya

Legit.ng ta samu kuma dai cewa jarumin ya bayyana cewa wakar da ya fara yi da ta sa shi yayi suna a duniyar Kannywood ita ce ta "Soyayya bazan kara Ba" da ya rere a fim din Sai Wata Rana.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa sabon jarumin shine ya jagoranci fim din nan da ya shahara a bakunan mutane da kuma bai dade da fitowa ba watau Mansoor na kamfanin FKD mallakar jarumi Ali Nuhu.

Kuma ya kara da cewa mutane na bukatan nishadi a finafinai, inda mawaka suka shigo kenan.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Watch Nigerian singer Simi perform tracks from her brand new album Simisola On Legit.ng TV

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHB9kGxnb2pnYrGiusOao6KmXaCur7rYsKaonF2ovLqt2LKYZpuVYsGiedKaZKeZXZuus62MsJikmV2quqK%2BjKZkrKCRp7Kmso2hq6ak